Fitaccen Sanatan dake kare muradun Trump da Isra’ila a Majalisar Amurka ya mutu ba zato ba tsammani

DA DUMI-DUMI

Abokin Kawancen Trump, Sanata Lindsey Graham Ya Rasu Yana da Shekara 71

Fitaccen Sanatan Amurka kuma na kusa da Shugaba Donald Trump, Lindsey Graham, ya rasu yana da shekara 71 bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a shafinsa na X a daren Asabar, an ce Lindsey Graham ya rasu ne sakamakon wata rashin lafiya da ta zo ba zato ba tsammani, yayin da iyalansa suka nemi a mutunta sirrinsu tare da yi musu addu’a.

An fara zaɓen Lindsey Graham zuwa Majalisar Wakilan Amurka a shekarar 1994, kafin daga bisani ya zama Sanata a shekarar 2002. Daga nan aka sake zaɓensa a shekarun 2008, 2014 da 2020, inda a baya-bayan nan yake jagorantar Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawan Amurka.

Gwamnan jihar South Carolina, Henry McMaster, ya bayyana Lindsey Graham a matsayin mutum “wanda ba za a iya maye gurbinsa ba,” yana mai cewa ya kasance jajirtaccen mai kare muradun jiharsa da Amurka.

Shi ma Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya ce ya kadu matuƙa da labarin rasuwar Lindsey Graham, yana yabawa gudummawar da ya bayar wajen ƙarfafa alaƙar Amurka da Isra’ila tare da goyon bayan da ya nuna wa ƙasar a lokutan ƙalubale.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img