Dan Wasan South Africa Jayden Adams Ya Mutu Jim Kaɗan Bayan Wakiltar Kasarsa a World Cup

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Dan wasan tsakiya na ƙungiyar Mamelodi Sundowns da kuma tawagar ƙasar South Africa, Jayden Adams, ya rasu yana da shekaru 25 a duniya.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin ‘Yan Wasan Kwallon Kafa ta South Africa (SAFPU) ce ta tabbatar da rasuwarsa a ranar Asabar, sai dai ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba.

Jayden Adams ya wakilci South Africa a wasanni uku na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, inda ya fara wasa a biyu daga cikinsu. Ya ci gaba da buga wa ƙasarsa wasa duk da rasuwar kakarsa, Marianna Adams, kwana guda kafin wasan da Czech Republic.

Kafin gasar ta duniya, Jayden Adams ya taimaka wa Mamelodi Sundowns lashe Gasar Zakarun Nahiyar Afirka (CAF Champions League), sannan ya sadaukar da lambar yabonsa ga tsohon abokin wasansa na Stellenbosch FC, Oshwin Andries, wanda aka kashe a 2023.

Ministan Wasanni, Fasaha da Al’adu na South Africa, Gayton McKenzie, ya bayyana rasuwar Jayden Adams a matsayin babban rashi ga ƙasar, yana mai cewa matashin ya nuna kishin ƙasa da jajircewa har zuwa ƙarshe.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img