“An kai wasu malamai Saudiyya domin yi wa gwamnati addu’ar zarcewa, amma da suka je sai suka roƙi rushewarta” – Sheikh Sunusi Khalil

DA DUMI-DUMI

“An kai wasu malamai Saudiyya domin yi wa gwamnati addu’ar zarcewa, amma da suka je sai suka roƙi rushewarta” – Sheikh Sunusi Khalil

Daga Wakiliya

Sheikh Sunusi Khalil ya bayyana cewa wasu malamai da aka kai Saudiyya domin yin addu’a kan sake zaɓen wasu shugabannin Najeriya, sun ce ba sake zaɓensu suke roƙa ba, illa addu’ar rushewar gwamnatin suke yi.

Sheikh Sunusi ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda yake gabatar da hudubar Juma’a.

A cewarsa, ya tattauna da ɗaya daga cikin malaman da aka kai Saudiyyar, inda ya tambaye shi yadda yake jin daɗin yin addu’ar sake zaɓen gwamnatin da yake kallonta a matsayin mai tsanani.

Sai ya ce malamin ya amsa masa da cewa ba sake zaɓen gwamnatin suke addu’a ba, suna addu’ar Allah ya kawo ƙarshenta ne.

Sheikh Sunusi ya ƙara da cewa abin da malamin ya bayyana masa ba abin dariya ba ne.

Sai dai bai bayyana sunayen malaman da ya ce an kai Saudiyya ba, ko kuma takamaiman gwamnatin da yake magana a kanta ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img