“Kaduna na fuskantar sabon salo na kyakkyawan shugabanci na cigaba mai cike da tausayi da jinƙan jama’a ƙarƙashin Uba Sani” – Gumi
Daga Wakiliya
Dr. Ahmed Mahmud Gumi ya yabawa Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, kan yadda ya ce gwamnatin jihar ke aiwatar da sauye-sauye a fannin mulki da ci gaban al’umma.
Gumi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa bayan halartar bikin ƙaddamar da aikin sabunta makarantar firamare ta Sultan Bello, makarantar da ya ce ya yi karatu a cikinta fiye da shekara 60 da ya wuce.
Ya ce aikin na daga cikin jerin ayyukan inganta ilimin bai-daya da ake gudanarwa a sassan jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani.
Gumi ya yaba wa Gwamnan bisa abin da ya bayyana a matsayin jajircewa wajen samar da ci gaba, yana mai cewa a ƙarƙashin gwamnatin Uba Sani, Kaduna na fuskantar wani sabon salo na shugabanci da kyakkyawan tsari wanda ya damu da jama’a.
A cewarsa, sabon salon mulkin ya mayar da jinƙai da walwalar ɗan Adam a matsayin ginshiƙan kyakkyawan shugabanci.
Gumi ya ce: “Ina yaba wa Gwamnan bisa jajircewarsa wajen kawo ci gaba. A ƙarƙashin gwamnatinsa, Kaduna na fuskantar wani babban sauyi a fannin kyakkyawan shugabanci, wanda ya sanya tausayi da jin kan ɗan Adam a tsakiyar komai.”




