Na je Italiya domin yin addu’a ga Najeriya, kan matsalolin rashin tsaro – Akpabio 

DA DUMI-DUMI

Na je Italiya domin yin addu’a ga Najeriya, musamman kan matsalolin rashin tsaro, ‘yan bindiga da ta’addanci -inji Akpabio

Daga Wakiliya

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ya je Italiya domin yin addu’a ga Najeriya, musamman kan matsalolin rashin tsaro, ‘yan bindiga da ta’addanci.

Akpabio ya bayyana cewa ya kai ziyara wurin ibadar St. Padre Pio da ke San Giovanni Rotondo, inda ya yi addu’a ga Najeriya da shugabanninta.

Ya ce addu’ar ta shafi Shugaba Bola Tinubu, da shi kansa, da mataimakin shugaban ƙasa, da ‘yan Majalisar Tarayya da sauran jami’an gwamnati.

Akpabio ya ce ya kuma roƙi Allah ya kawo ƙarshen rashin tsaro, ‘yan bindiga da ta’addanci a Najeriya.

Ya bayyana tafiyar a matsayin wata gajeriyar ziyarar ibada, yana mai cewa a imaninsa, ƙoƙarin ɗan Adam ba ya wadatarwa sai da kariyar Allah.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img