AN fara Zargin FIFA da Nuna Son Kai Ga Messi Da Argentina a gasar world cup

Daga Wakiliya

Ana ci gaba da taƙaddama a kafafen sada zumunta yayin da wasu magoya baya ke zargin FIFA da nuna son kai ga Argentina da tauraron ƙwallonta, Lionel Messi, kafin wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya da Spain.

Zargin ya ƙaru ne bayan nasarar da Argentina ta samu a kan Masar, inda masu sukar suka ce wasu hukunce-hukuncen alƙalai sun fifita Argentina. Kocin Masar, Hossam Hassan, ya bayyana wasan a matsayin “rashin adalci”, yana mai cewa wasu hukuncin alƙalai sun cutar da ƙungiyarsa, har ya yi zargin cewa FIFA na son Messi ya ci gaba da zama a gasar.

Sai dai kocin Argentina, Lionel Scaloni, ya musanta zarge-zargen, yana cewa irin waɗannan maganganu sun daɗe ana yi kan Argentina, kuma babu wata hujja da ke nuna FIFA tana nuna masu son kai. Haka kuma shugaban alƙalan FIFA, Pierluigi Collina, ya ce babu wanda zai iya yin tasiri kan alƙalan FIFA, ko da shugaban FIFA Gianni Infantino ne.

A kafafen sada zumunta kuwa, an yaɗa hotuna da bidiyoyi da ke zargin FIFA da fifita Messi, ciki har da wasu da aka ƙirƙira da fasahar AI, yayin da wasu sakonni suka yi ikirarin ba tare da hujja ba cewa Messi ya biya kuɗi domin samun ƙarin bugun fenariti.

Messi, wanda Forbes ta kiyasta arzikinsa ya kai dala biliyan 1.1, ya zura ƙwallaye takwas a gasar bana, abin da ya sa yake kan gaba wajen cin ƙwallaye tare da Kylian Mbappe na Faransa.

Argentina za ta kara da Spain a wasan ƙarshe na gasar ranar Lahadi a filin wasa na MetLife da ke jihar New Jersey, Amurka.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img