$38bn: Arzikina Ya Fi Abin da Mujallar Forbes Ke Nunawa -inji Dangote

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya ce dukiyar da ake dangantawa da shi cewa ta kai dala biliyan 38 ba ita ce cikakkiyar darajar arzikinsa ba.

A wata hira da ya yi, Dangote ya bayyana cewa yawancin manyan kamfanoninsa ba a jera su a kasuwannin hannayen jari ba, lamarin da ya nuna ƙididdigar Forbes da Bloomberg ba ta nuna ainihin girman dukiyarsa ba.

“Sun ce ina da dala biliyan 38, amma mafi yawan kasuwancinmu ba a lissafa su ba tukuna. Nan gaba za a ga hakikanin darajarsu,” in ji shi.

Dangote ya ce kamfanonin da ba a jera ba, musamman Matatar Mai ta Dangote da kuma kamfanin taki, suna daga cikin manyan kadarorinsa masu matuƙar daraja.

Ana sa ran Matatar Mai ta Dangote za ta shiga kasuwar hannayen jari nan gaba, a wani mataki da masana ke hasashen zai zama mafi girman IPO da aka taɓa yi a nahiyar Afirka.

Masana sun kiyasta darajar matatar tsakanin dala biliyan 25 zuwa 30, abin da ka iya ƙara ɗaga matsayin Dangote a jerin attajiran duniya.Rahoton Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img