Daga Wakiliya
Kasuwar man fetur ta duniya na fuskantar sabon ƙalubale bayan rahotanni sun nuna cewa sama da gangar mai biliyan 1.15 ta ɓace daga kasuwa sakamakon rikicin da ya ɗauki watanni tsakanin Iran da Amurka.
Ko da yake an sake buɗe mashigin Hormuz bayan cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu, masana sun yi gargadin cewa dawo da harkokin mai yadda suke a baya na iya ɗaukar watanni masu yawa.
Rahotanni sun nuna cewa ajiyar mai na gaggawa a ƙasashe da dama sun ragu zuwa mafi ƙarancin mataki cikin shekaru da dama, yayin da wasu manyan wuraren ajiyar mai ke fuskantar matsalar ƙarancin haja.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce duniya na iya shiga matsanancin rikicin tattalin arziki idan ba a dawo da wadataccen mai kasuwa cikin lokaci ba.
Duk da saukar farashin danyen mai daga sama da dala 126 zuwa ƙasa da dala 80 kan kowace ganga bayan yarjejeniyar, wasu masana na ganin kasuwa ta yi gaggawar sauka, alhali har yanzu akwai babbar matsala wajen dawo da isasshen mai.
Sai dai wasu masana na ganin cewa ƙasashen OPEC da sauran masu samar da mai za su iya ƙara yawan samarwa cikin sauri, lamarin da zai taimaka wajen rage matsin lambar da ake fuskanta.
Masu nazari sun ce makonni da watanni masu zuwa za su nuna ko duniya za ta fuskanci sabon tashin farashin mai ko kuma samar da mai zai dawo yadda ake buƙata.
Rahotan Wakiliya





