‘Yan Asalin Najeriya 16 Dake Buga Wa Wasu Ƙasashe A Gasar Kofin Duniya Ta 2026

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Duk da cewa Super Eagles ba ta samu tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 ba, har yanzu tasirin Najeriya na ci gaba da bayyana a gasar ta hanyar ‘yan wasa masu asalin Najeriya da ke wakiltar wasu ƙasashe.

Jimillar ‘yan wasa 16 masu asalin Najeriya ne ke fafatawa a gasar ƙarƙashin tutocin ƙasashe tara daban-daban, lamarin da ke nuna yadda hazikan ‘yan wasan Najeriya suka bazu a faɗin duniya.

Daga cikin fitattun sunayen akwai Bukayo Saka, Eberechi Eze da Noni Madueke da ke bugawa Ingila, Michael Olise na Faransa, Folarin Balogun na Amurka, Jamal Musiala da Felix Nmecha na Jamus.

Haka kuma akwai David Alaba da Carney Chukwuemeka na Austria, Manuel Akanji da Noah Okafor na Switzerland, yayin da Tani Oluwaseyi, Promise David da Owen Goodman ke wakiltar Canada.

Sauran sun haɗa da Ime Okon na Afirka ta Kudu da kuma Antonio Nusa na Norway.

Rashin ganin Najeriya a gasar ya kasance abin takaici ga magoya baya, amma kasancewar waɗannan ‘yan wasa masu jinin Najeriya a manyan ƙasashen duniya na nuna irin gudunmawar da Najeriya ke ci gaba da bayarwa ga ƙwallon ƙafa ta duniya.

Wakiliya: Ko da Super Eagles ba ta halarta ba, jinin Najeriya na ci gaba da haskakawa a babban filin wasan ƙwallon ƙafa na duniya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img