Wata Sabuwa: CFRPA Ta Bukaci INEC Ta Binciki Takardun Karatun Tinubu

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Wata ƙungiyar farar hula mai suna Center for Reform and Public Advocacy (CFRPA) ta miƙa koke ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), tana neman a sake binciken sahihancin takardun karatun Tinubu ya gabatar yayin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A cikin koken da aka aika ranar 19 ga Yuni, ƙungiyar ta buƙaci INEC ta yi bayani kan sahihancin takardar shaidar kammala karatu daga Jami’ar Chicago State University (CSU) da Tinubu ya gabatar.

Masu koken sun yi zargin cewa akwai saɓani a bayanan makarantar da aka ambata a takardun shiga jami’ar, tare da cewa akwai buƙatar ƙarin bincike kan wasu takardun karatu da na NYSC da aka danganta da shugaban ƙasar.

Ƙungiyar ta ce idan INEC ba ta fito da matsayinta kan lamarin ba, za ta ɗauki matakin shari’a domin hana karɓar takarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, INEC da Fadar Shugaban Ƙasa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan sabon koken ba.Rahoton Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img