Wani abu da ake zargin Bom ne ya tashi a babbar kasuwar  Lagos

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta tabbatar da faruwar wata fashewa da ake zargin bam na gida (IED) ne ya haddasa a Kasuwar Kayan Takalma da ke Mushin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Fatai Tijani, ya ce an boye abin fashewar ne a karkashin kujerar fasinja ta wata mota, inda ya tashi lokacin da aka kunna motar.

A cewarsa, mutum daya ne ya samu raunuka kuma an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa, inda aka tabbatar da cewa halin da yake ciki yana da kyau.

Tijani ya ce jami’an kwantar da bama-bamai sun gudanar da bincike a wurin, kuma ba su gano wani karin abin fashewa ba.

Ya bukaci mazauna yankin da ‘yan kasuwa su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, yana mai tabbatar da cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img