Daga Wakiliya
Wani mutum mai suna Rogelio Andaverde ya jefa jami’an tsaro cikin ruÉ—ani bayan ya shirya a yi kamar an yi garkuwa da shi domin ya samu damar fita yawon shakatawa tare da abokansa ba tare da ya yi wa matarsa bayani ba.
Lamarin ya faru ne a daren 1 ga Oktoba, 2013, a garin Edinburg na jihar Texas a Amurka. Rahotanni sun ce wasu abokansa biyu, sanye da abin rufe fuska kuma dauke da bindigogin bogi, sun kutsa gidansa tare da fitar da shi da ƙarfi a gaban matarsa Maria Andaverde.
Cikin firgici, Maria ta kira lambar gaggawa ta 911, inda ta sanar da cewa an yi garkuwa da mijinta. Hakan ya sa jami’an Hidalgo County Sheriff’s Office suka kaddamar da gagarumin bincike, tare da amfani da jirgin sama mai saukar ungulu na Texas Department of Public Safety wajen neman sa.
Sai dai bayan kwana biyu, Rogelio Andaverde ya dawo gida lafiya, yana ikirarin cewa wadanda suka sace shi ne suka sake shi.
Bayan jami’an tsaro sun yi masa tambayoyi, Rogelio Andaverde ya amsa cewa shi ne ya shirya wannan wasan kwaikwayon domin kawai ya fita ya yi walwala tare da abokansa ba tare da samun matsala daga matarsa ba.
Daga bisani an gurfanar da Rogelio Andaverde a kotu bisa laifin bayar da rahoton Æ™arya ga jami’an tsaro, inda daga baya ya amsa laifinsa.





