Burkina Faso Ba Za Ta Karɓi Shari’ar Musulunci A Matsayin Tsarin Mulki Ba, Gwara Ku Koyi Kimiyya da Fasaha – Traoré

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya sake jaddada cewa ƙasar sa za ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai bai wa kowa ‘yancin addininsa, yana mai cewa Shari’ar Musulunci ba za ta zama tsarin mulkin Burkina Faso ba.

Traoré ya bayyana cewa duk da kasancewarsa Musulmi, gwamnati ba za ta amince da wani tsarin addini da zai maye gurbin dokokin ƙasa ba. Ya kuma yi kira ga ɗaliban Burkina Faso da ke karatun Shari’a a ƙasashen waje da su mayar da hankali kan ilimin fasaha, kimiyya da sana’o’in da za su taimaka wajen bunƙasa ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa Traoré ya soki yadda ɗaruruwan ɗaliban Burkina Faso ke karatun Shari’a a Saudiyya ba tare da cikakken rajista a ofishin jakadancin ƙasar ba, yana tambayar inda suke sa ran amfani da irin wannan ilimi idan suka dawo gida.

Sai dai bincike ya nuna cewa wasu kalaman da ake yaɗawa a shafukan sada zumunt, musamman ikirarin cewa gwamnatin ta haramta wa duk ɗaliban Shari’a komawa Burkina Faso ko kuma za ta ƙwace musu ɗan ƙasa, ba a samu tabbatacciyar sanarwar gwamnati ko cikakken rubutaccen jawabi da ya tabbatar da hakan ba. Abin da aka tabbatar shi ne Traoré ya yi amfani da kalamai masu tsauri wajen sukar karatun Shari’a a ƙasashen waje tare da fifita ilimin fasaha da ci gaban ƙasa.

Wannan matsaya na zuwa ne yayin da Burkina Faso ke ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da gwamnati ke zargi da amfani da addini wajen tayar da ta’addanci, tare da ƙaddamar da sabbin dokoki domin dakile tsattsauran ra’ayi da kare haɗin kan al’umma.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img