Wani mutum ya mutu bayan ya shiga otel da matar aure a Abuja – ana zargin matar ta gudu da wayarsa

DA DUMI-DUMI

Wani mutum ya mutu bayan ya shiga otel da matar aure a Abuja – ana zargin matar ta gudu da wayarsa

Daga Wakiliya

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa wani mutum ya mutu a cikin wani ɗakin otel da ke Gwarimpa, Abuja, bayan ya shiga otel ɗin tare da wata matar aure.

A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa matar ta bar otel ɗin bayan ta gano cewa mutumin ya daina numfashi, inda ake zargin ta tafi da wayarsa.

Daga bisani, ma’aikatan otel ɗin sun gano gawar mutumin. Sai dai rundunar ta ce maimakon su sanar da ’yan sanda, sai wasu ma’aikatan otel din su biyu, Ibrahim Omeiza da Kefat Bitrus, suka ɗauki gawar daga otel ɗin tare da jefar da ita a ƙarƙashin gadar Katampe.

Rundunar ’yan sandan ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutumin da kuma cikakken abin da ya faru.

Ta kuma ce duk wanda bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img