’Yan sanda a Abuja sun kama wani mutum yana yi wa yarinya ’yar shekara 12 fyade a mota – daga baya aka gano tana ɗauke da cikin wata Uku
Daga Wakiliya
Rundunar ’yan sandan Abuja ta ce ta kama wani mutum mai suna Zayyanu Halilu bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade a cikin mota.
Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce ’yan sandan sun gano lamarin ne yayin da suke sintiri a kusa da Airport Bridge Taxi Park, inda suka ga wata mota mai tintet tana motsi ita kadai duk da cewa tana ajiye ne.
Ta ce jami’an sun bude motar, inda suka tarar da wanda ake zargin yana yi wa yarinyar fyade, sannan suka ceto ta tare da kama wanda ake zargin.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargain ya sha lalata da yarinyar a cikin motar, inda ya ke yi mata barazanar kada ta faɗawa kowa.
’Yan sanda sun ce binciken lafiya ya nuna cewa yarinyar tana da ciki na kusan watanni uku, wanda ake zargin ya samo asali ne daga lalata da ya yi da ita.
Rundunar ta ce yarinyar na samun kulawar likitoci, yayin da wanda ake zargin ke hannun ’yan sanda kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.




