An dakatar da kisan wata fursunar Amurka bayan an yi mata allurar kisa har sau Biyu amma taki mutuwa

DA DUMI-DUMI

An dakatar da kisan wata fursunar Amurka bayan an yi mata allurar kisa har sau Biyu amma taki mutuwa

Daga Wakiliya

Wata fursunar da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Tennessee ta Amurka, Christa Pike, ta ci gaba da rayuwa bayan an yi mata allurar kisa har sau biyu amma ta ki mutuwa, kamar yadda lauyoyinta suka bayyana.

Lauyoyin Pike sun ce bayan an yi mata allurar pentobarbital, sai aka ga har bayan wajen awa guda tana numfashi kuma zuciyar ta na cigaba da bugawa, yayin da take kuma yin gyatsa.

Rahotanni sun ce bayan ganin taki mutuwa sai jami’an gidan yarin suka sauke labulen dakin kisan, sannan daga bisani aka fitar da ‘yan jaridun da aka ba damar kallon kisan.

An samu Pike da laifin kashe abokiyar karatunta, Colleen Slemmer, a shekarar 1995. Ta yi amfani da wani abin yanka da kuma gatari wajen kai mata hari da kashe margayiyar, a wani kisa da kotu ta bayyana cewa ya yi matukar muni.

Shekara kusan fiye da 30 kenan ana tsare da Pike kafin yanzu aka yi yunƙurin zartar da hukuncin kisan kuma abu ya gagara lamarin da ya jawo aka garzaya da ita asibiti

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img