“Ya kamata a ƙara kuɗin makaranta zuwa aƙalla Naira miliyan ɗaya idan ana son jami’o’in Najeriya su inganta” – Olatunji-Bello

DA DUMI-DUMI

“Sai an ƙara kuɗin makaranta zuwa Naira miliyan ɗaya kafin jami’o’in gwamnati za su samu ci gaba” – Farfesa Olatunji-Bello

Daga Wakiliya

Tsohuwar shugabar Jami’ar Jihar Legas (LASU), Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello, ta ce jami’o’in gwamnati na Najeriya na bukatar ƙara kuɗin makaranta zuwa aƙalla Naira miliyan ɗaya ga kowane ɗalibi domin samun cikakkiyar dogaro da kai ta fuskar kuɗi.

Wakiliya ta ruwaito a wata hira da jaridar Punch, Olatunji-Bello, wadda ta kammala wa’adin mulkinta na shekaru biyar a ranar Asabar, ta ce jami’o’i na fuskantar tsadar gudanar da ayyuka, ciki har da albashi, wutar lantarki, tsaro da kula da muhalli.

Ta ce LASU na kashe sama da Naira biliyan ɗaya a wata wajen biyan albashi, yayin da kuɗin wutar lantarki kaɗai ya kai kusan Naira miliyan 140 a wata.

Ta ce duk da cewa ta ƙara kuɗin shiga na cikin gida na LASU daga Naira biliyan uku zuwa biliyan 13, kuɗin bai isa jami’ar ta dogara da kanta gaba ɗaya ba.

“Jami’ar gwamnati da ke son samun cikakken ’yancin kuɗi dole ta karɓi kuɗin makaranta da bai gaza Naira miliyan ɗaya ga kowane ɗalibi ba,” in ji ta.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img