Wike ya bayyana dalilin da bai halarci jana’izar mahaifiyar Amaechi ba
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa bai halarci jana’izar mahaifiyar tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, ba, saboda bai samu labarin rasuwar ba daga Amaechi.
Wike ya ce yana tsammanin Amaechi zai tuntube shi domin sanar da shi rasuwar mahaifiyarsa, amma hakan bai faru ba.
“Ina tsammanin Amaechi zai rubuto mini ya sanar da ni rasuwar mahaifiyarsa, amma bai rubuto mini ko ya sanar da ni cewa ya rasa mahaifiyarsa ba.
“Duk abin da ya faru a ranar jana’izar ya faru ne saboda ban san abin da ke faruwa ba,” in ji Wike.
Ya kuma ce rashin halartarsa jana’izar da kuma rashin aika saƙon ta’aziyya ba ya da alaƙa da wani dalili daban, illa kasancewar bai samu labarin rasuwar ba.




