Daga Wakiliya
Wata mata mai suna Kendra Scott mai shekaru 36 ta shiga hannu bayan ana zarginta da harbe tare da kashe wani matashi mai shekaru 20, Rodderius Morton, a harabar gidanta da ke birnin Memphis na jihar Tennessee, Amurka.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar Alhamis, lokacin da Kendra Scott ta dawo gida tana buga ƙofa tare da ihu tana tambayar, “Wa yake cikin gidana?” kafin ta shiga ɗauke da bindiga.
‘Yar Kendra Scott, wadda ba a bayyana sunanta ba saboda ƙarancinta, ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta shigar da Rodderius Morton cikin gidan ta ƙofar baya bayan ƙarfe 1:00 na dare. Da mahaifiyarta ta dawo, Morton ya ɓoye a ƙarƙashin gadonta saboda tsoro.
Rahoton ‘yan sanda ya ce yarinyar ta bayyana cewa mahaifiyarta ta taɓa faɗa mata cewa za ta harbe duk wani saurayi da ta kama a cikin gidan.
Bayan Morton ya fito daga ƙarƙashin gadon domin ya tattara kayansa ya bar gidan, Kendra Scott ta ci gaba da binsa tana masa ihu ya fita. Ana zargin cewa, duk da Morton ba shi da makami, ta harbe shi sau ɗaya a bayan kansa yayin da yake ƙoƙarin ficewa.
Jami’an ‘yan sanda sun tarar da gawarsa a farfajiyar gidan kusa da barandar shiga.
Wani maƙwabci ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya ga Kendra Scott ta shiga gidan da bindiga, sannan ya ji karar harbi guda ɗaya. Daga baya kuma ya ji tana maimaita cewa, “Na harbe shi.”
A cewar takardar tuhumar, Kendra Scott ta shaida wa jami’an tsaro cewa: “Na ga wani mutum a ƙarƙashin gadon ‘yata, kuma na yi abin da ya dace.”
Yanzu haka an gurfanar da Kendra Scott bisa zargin kisan kai na mataki na farko da kuma amfani da bindiga wajen aikata babban laifi.





