Neman kusanci da Isra’ila ya sa Najeriya ta sauya matsayinta kan Falasdinu – MPAC ta soki Tinubu

DA DUMI-DUMI

Neman kusanci da Isra’ila ya sa Najeriya ta sauya matsayinta kan Falasdinu – MPAC ta soki Tinubu kan rashin ambaton Gaza a UNGA 2026

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta Najeriya ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan rashin ambaton Falasdinu da Gaza a jawabin Najeriya na taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 2026.

MPAC ta ce jawabin mai sakin layi 24 ya tattauna batutuwa da dama, ciki har da sauyin yanayi, basussukan ƙasashe da yaƙi da ta’addanci, amma bai ambaci Falasdinu ko batun kafa ƙasashe biyu ba.

Ƙungiyar ta ce hakan ya bambanta da matsayin Najeriya a taron UNGA na bara, inda ta bayyana goyon bayanta ga samar da ƙasashen Falasdinu da Isra’ila a matsayin ƙasashe biyu.

MPAC ta danganta sauyin da ƙara ƙarfafa dangantakar tsaro da diflomasiyya tsakanin Najeriya da Isra’ila, tare da yin kira ga gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin sauyin matsayinta kan Falasdinu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img