Daga Wakiliya
A ranar 6 ga Maris, 1981, an ga wani abin mamaki a kotun birnin Lübeck da ke Yammacin Jamus,
Marianne Bachmeier, mai shekaru 30, ta halarci shari’ar Klaus Grabowski, mutumin da ake tuhuma da yi wa ‘yarta Anna Bachmeier mai shekara 7 fyade tare da kashe ta.
Yayin da shari’ar ke gudana, Marianne ta fitar da ƙaramar bindiga da ta ɓoye, ta harbi Grabowski sau da dama a cikin kotu, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take a gaban alkalai, lauyoyi da ‘yan jarida.
Bayan harbin, an ruwaito cewa Marianne ta ce: “Na yi hakan ne saboda ke, Anna.”
Bincike ya nuna cewa Grabowski ya taɓa samun hukunci a baya kan laifukan lalata da yara. Ya amsa kashe Anna, amma wasu kalaman da ya furta a kotu sun ƙara fusata mahaifiyar yarinyar.
Daga baya kotu ta gurfanar da Marianne. An same ta da laifin kashe kai ba tare da shirin kisa ba (manslaughter) da kuma mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba. An yanke mata hukuncin daurin shekara shida, amma ta shafe kusan shekara uku a gidan yari kafin a sake ta.
Lamarin ya raba kan al’ummar Jamus. Wasu sun ɗauke ta a matsayin uwa da baƙin ciki ya rinjaya, yayin da wasu suka ce abin da ta yi ya saba wa doka kuma bai kamata mutane su riƙa ɗaukar doka a hannunsu ba.
Marianne Bachmeier ta rasu a shekarar 1996 tana da shekaru 46 bayan fama da cutar sankarar pancreas.





