Dara Ta Ci Gida: ‘Yan Sanda a Shingen Bincike Sun Tare Shugaban ICPC, Sun Tilasta Masa Ciro N53,000 Ta POS Ba Tare da Sun San Shi Ba

Daga Wakiliya

Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta cafke wasu jami’anta huɗu da ake zargi da karɓar cin hanci da ƙwace wa Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Dr. Musa Aliyu (SAN), kuɗi har Naira 53,000 a wani shingen bincike da suka kafa ba bisa ƙa’ida ba a yankin Banex da ke Wuse, Abuja.

Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT, Ahmed Sanusi, ya bayyana cewa jami’an sun bar wuraren aikinsu, suka haɗu suka kafa shingen bincike domin karɓar kuɗi daga masu ababen hawa, ba tare da sun san cewa mutumin da suka tare shi ne shugaban ICPC ba.

A cewarsa, jami’an sun tilasta wa Dr. Musa Aliyu cire Naira 53,000 ta hanyar POS, har ma ya biya kuɗin cajin cire kuɗin, kafin suka raba kuɗin a tsakaninsu.

Ahmed Sanusi ya bayyana jami’an a matsayin “ɓarayi da ba su cancanci sanya kayan aikin ‘yan sanda ba,” yana mai cewa an kama dukkansu kuma za a hukunta su, inda ya ce waɗanda suka cancanci kora daga aiki za a kore su.

Kwamishinan ya kuma sake jaddada umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda cewa babu wani jami’i da ke da ikon tsayar da mutum a hanya ya tilasta masa miƙa wayarsa domin bincike. Ya buƙaci jama’a su ƙi amincewa da irin wannan buƙata, sannan su gaggauta kai rahoto ga rundunar ‘yan sanda idan hakan ta faru.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img