Shekera Biyu da Aure, miji ya saki matarsa yar shekara 19 ba faɗa ba komi wai kawai “ya gaji” da auren

DA DUMI-DUMI

Shekera Biyu da Aure, miji ya saki matarsa yar shekara 19 ba faɗa ba komi kawai “ya gaji” da auren

Daga Wakiliya

Ta yaya kalmar “na gaji” za ta zama dalilin da namiji zai saki matarsa, musamman yarinya ‘yar shekara 19 da ta haifa masa ɗa guda?

Wannan shi ne abin da ya faru da wata budurwa, wadda mijinta ya mayar da ita gidan iyayenta bayan sun shafe kusan shekaru biyu da aure.

Iyayenta sun tambayi mijin ko yarinyar ta aikata wani abu da ya sa ya yanke shawarar rabuwa da ita, domin idan akwai kuskure, su gyara mata kuma su ba ta shawara.

Amma mijin ya ci gaba da cewa kawai “ya gaji da auren”, ba tare da bayyana ainihin abin da ya gajiyar da shi ba.

Mahaifin yarinyar ya kuma tambaye ta ko ta taɓa yi wa mijinta wani laifi ko kuma an samu wata matsala ko rashin fahimta a tsakaninsu.

Sai ta bayyana cewa ba ta taɓa yi masa wani laifi ba, kuma babu wata babbar matsala ko rashin fahimta da ta faru tsakaninsu.

Abin tambaya shi ne: Shin “na gaji” kaɗai ya isa ya zama dalilin wargaza aure, musamman bayan an haifi ɗa kuma yarinyar tana da shekaru 19 kacal?

Idan da ɗiyarku ce ko ƙanwarku, kuma mijinta ya sake ta ba tare da ya bayyana wani takamaiman dalili ba, me za ku yi?

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img