Gwamnatin Kano za ta samar da wuraren cajin motocin lantarki a birnin Kano

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Kano za ta samar da wuraren cajin motocin lantarki a birnin Kano

Daga Wakiliya

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin samar da wuraren cajin motocin lantarki a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta na jihar, Mohammed Taju Usman, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Talata.

Kwamishinan ya ce shirin zai fara ne a matsayin aikin gwaji, tare da fatan faɗaɗa shi zuwa wasu wurare a jihar idan aka samu nasara.

Ya bayyana cewa samar da wuraren cajin motocin lantarki na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka wajen bunƙasa amfani da fasahar zamani da kuma samar da abubuwan more rayuwa da suka dace da sauye-sauyen da ake samu a harkokin sufuri.

Sai dai gwamnatin jihar ba ta bayyana takamaiman wuraren da za a kafa tashoshin cajin ba, ko kuma lokacin da za a fara aikin ba.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da amfani da motocin lantarki ke ƙara samun karɓuwa a sassa daban-daban na duniya, sakamakon ƙoƙarin rage dogaro da man fetur da kuma rage gurɓatar muhalli.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img