Daga Wakiliya
Kotun Amurka ta umarci fitaccen mawaki Chris Brown da kamfaninsa Black Pyramid LLC su biya kimanin dala miliyan 13 diyya ga tsohuwar ma’aikaciyar gidansa, Maria Avila, bayan kare da ke gidansa ya kai mata hari a shekarar 2020.
Alkalai sun yanke hukuncin ne bayan shari’ar da ta ɗauki makonni biyu a birnin Los Angeles, inda suka tabbatar da cewa Brown ya yi sakaci wajen kare lafiyar ma’aikaciyar.
Maria Avila ta shaida wa kotu cewa karen mai suna Hades ya yi mata munanan raunuka, lamarin da ya jawo mata tabo na dindindin a fuska da hannu, lalacewar gani da kuma matsalar jijiyoyi.
A yayin shari’ar, an kuma bayyana cewa Chris Brown ya bar wurin da lamarin ya faru maimakon ya kira jami’an gaggawa, inda ya ce ya ji tsoron kafofin watsa labarai su mamaye wurin.
Sai dai Brown ya musanta cewa karen nasa ne kai tsaye, yana mai cewa jami’an tsaronsa ne ke kula da shi domin kare gidan daga masu kutse.
Baya ga diyyar da aka bai wa Maria Avila, kotu ta kuma ba wa ‘yar uwarta Patricia Avila dala 885,000, yayin da mijinta Oscar Olivo ya samu dala 50,000.
Chris Brown na ci gaba da rangadin wakokinsa a Amurka, yayin da kuma ake sa ran zai sake gurfana a wata kotu a Birtaniya a watan Oktoba kan zargin kai hari ga wani furodusan kiɗa a shekarar 2023.





