Daga Wakiliya
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin aiki na bankunan kananan yan kasuwa da bayar da rance, Microfinance guda 46 saboda gaza cika wasu Æ™a’idojin da ake buÆ™ata domin ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Mai magana da yawun CBN, Hakama Sidi-Ali, ta bayyana a ranar Laraba cewa matakin ya fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026, bisa tanade-tanaden Dokar BOFIA ta 2020.
Daga cikin bankunan da abin ya shafa akwai Bompai MFB, Minjibir MFB, Shanono MFB, Sumaila MFB, Rimin Gado MFB, Tofa MFB, Kanopoly MFB, Bellbank MFB (tsohon Tsanyawa MFB), Basawa MFB, Zain MFB (tsohon Dawakin Tofa MFB) da wasu da dama, inda rahotanni ke nuna cewa mafi yawansu suna Arewacin Najeriya.
CBN ta ce an É—auki wannan mataki ne domin tabbatar da bin Æ™a’idojin tsarin banki da kare lafiyar harkokin kuÉ—i a Æ™asar.
Ga su kamar haka:-
1. Minji-Se Churchill MFB
2. Merchant MFB
3. Janmaa MFB
4. Busu MFB
5. Gold MFB
6. Zain MFB (formerly Dawakin Tofa MFB)
7. Bompai MFB
8. Ajwa MFB (Formerly Gezawa)
9. NOW NOW DIGITAL MFB
10. Crystabel Microfinance Bank
11. Chanelle MFB
12. Abia SME MFB
13. Kamba MFB
14. Iwade MFB
15. Winview MFB
16. Zuru MFB
17. Minjibir MFB
18. Shanono MFB
19. Sumaila MFB
20. Rimin Gado MFB
21. Mwaghavul MFB
22. Sycamore MFB
23. TOFA MFB
24. Safegate MFB
25. Creekline MFB
26. Bestar MFB
27. Livingspring MFB
28. Apple MFB
29. Stanford MFB
30. Frontline MFB
31. Zafec MFB
32. Supreme MFB
33. Bejin-Doko MFB
34. Kanopoly MFB
35. Bellbank MFB (formerly Tsanyawa)
36. Yeneng MFB
37. Creditville MFB
38. MBAG MFB
39. STRAIGHT SAHARA MFB
40. OURPASS MFB
41. VERDANT MFB
42. BASAWA MFB
43. CASHA MFB
44. ESTEEM MFB
45. ENTREPRENEUR MFB
46. AVANTUS MFB





