Kotu ta tura wani matashi gidan yari bisa zargin yin bidiyo kan Tinubu da ɗansa Seyi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Wata Kotun Majistare da ke yankin Ogba a Jihar Legas ta ba da umarnin tsare fitaccen mai ƙirƙirar abubuwan nishaɗi a kafafen sada zumunta, DJ Chicken, a gidan yarin Kirikiri har sai ya cika sharuɗɗan belinsa.

An gurfanar da DJ Chicken ne kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da karya dokar laifukan yanar gizo (Cybercrimes Act), tayar da zaune tsaye da kuma yi wa Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, barazanar kisa.

Lamarin ya biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda DJ Chicken ya ce Shugaba Tinubu ba zai ci zaɓen 2027 ba, tare da yin barazanar kashe Seyi Tinubu idan shugaban ya sake lashe zaɓe.

Daga baya DJ Chicken ya janye kalamansa, yana mai cewa wasa ne kawai da ya yi domin neman farin jini. Duk da haka, jami’an ‘yan sanda sun kama shi tare da gurfanar da shi a kotu.

Ko da yake ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, kotun ta ba shi beli kan kuɗi Naira miliyan ɗaya, tare da sharuɗɗan gabatar da masu tsaya masa biyu. Daya daga cikin masu belin dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati, ɗayan kuma jagoran al’umma mai kadarar ƙasa a Jihar Legas, yayin da ɗaya daga cikinsu dole ne ya kasance ɗan uwansa na jini.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Agusta, 2026, tare da umarnin ci gaba da tsare DJ Chicken a gidan yarin Kirikiri har sai ya cika dukkan sharuɗɗan belin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img