Kamfanin Amurka ya ƙera riga da ba ta bukatar wanki har na tsawon wata guda
Daga Wakiliya
Wani kamfanin kera tufafi da ke Amurka, HercLeon, ya ƙera wata sabuwar riga mai suna HercShirt V5.0, wadda ya ce mutum na iya sanya ta kullum tsawon kwanaki 30 ba tare da ya wanke ta ba.
Kamfanin ya ce rigar tana iya kasancewa ba tare da wari ba na tsawon wata guda, ko da ana amfani da ita sosai.
HercLeon ya ce ya yi amfani da wasu sinadarai guda bakwai wajen ƙera rigar, ciki har da tagulla, azurfa, zinc, zinariya da toka daga dutsen mai aman wuta, yayin da ya ce akwai wasu sinadarai biyu da bai bayyana sunayensu ba.
A cewar kamfanin, tagulla na taimakawa wajen dakile ƙwayoyin cuta da ke haddasa wari, yayin da zinc ke taimakawa wajen rage wasu sinadarai masu wari da ke fitowa yayin zufa.
Haka kuma, kamfanin ya ce tokar dutsen mai aman wuta na taimakawa wajen shan danshi da wasu warin da ke wajen jiki.
HercLeon, wanda a baya ya ƙera kayan sawa da ya ce suna taimakawa wajen rage wari, ya bayyana HercShirt V5.0 a matsayin rigar da za ta iya daɗewa fiye da rigunan da ake wankewa akai-akai.
Kamfanin ya ce za a fara jigilar rigar a farkon watan Nuwamba, inda za a fara samun ta da launin baki, kafin daga bisani a ƙara launuka irin su shuɗi mai duhu, burgundy da kore mai duhu.
Farashin rigar zai fara daga dala 39, yayin da samfurin HercShirt V5.0 zai kai dala 79.
Sai dai kamfanin ya ce samfurin dala 39 na iya kasancewa ba tare da wari ba har na tsawon kwanaki uku na amfani mai yawa, yayin da wani samfurin na tsaka-tsaki zai iya ɗaukar har zuwa kwanaki 14 ba tare da wanki ba.




