Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Duk wanda ya ce ’yan Najeriya na shan wahala ƙarƙashin Tinubu, ƙarya yake -mutanen da a baya ba sa iya sayen abinci yanzu suna iya saya -Abu Ammar Shugaban Hisbah na Katsina

Daga Wakiliya

Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Malam Abu Ammar, ya ce ba gaskiya ba ne cewa ’yan Najeriya na fama da matsananciyar wahala a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Malam Abu Ammar ya ce yanayin rayuwa ya inganta a wasu fannoni, inda ya ƙara da cewa mutanen da a baya ba sa iya sayen abinci yanzu suna iya saya.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, shugaban Hisbah ɗin ya ce ya ziyarci Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma kwanaki biyu da suka wuce, inda wasu malamai suka shaida masa cewa su da iyalansu suna godiya ga Shugaba Tinubu saboda wasu matakan da gwamnatin ta ɗauka a fannin ilimi.

Ya ce malamai da ɗaliban jami’o’i na daga cikin waɗanda suka san abin da ya kira “alherin” da ya samu ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

“Idan yunwa ba ta kashe mu ba, wace irin yunwa ce za mu ce muna magana a kanta? Ba mu da abin da za mu koka a kai,” in ji shi.

Malam Abu Ammar ya kuma ce malamai a manyan makarantun Najeriya ba su da wani abin da ya fi gabansu kamar Shugaba Tinubu, yana mai gargadin masu sukar gwamnati da kada su mayar da batun siyasa.

Ya ce idan gwamnati ta yi abin kirki, ya kamata ’yan Najeriya su nuna godiya maimakon nuna rashin godiya

DA DUMI-DUMI

Har yanzu Atiku, da Obi da Kwankwaso na da damar hada kai domin kawar da Tinubu a 2027 -Ologbondiyan

Ya ce burin ADC shi ne samar da gwamnati da za ta yi aiki domin amfanin ’yan Najeriya tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta amfani al’umma.

Kamfanin Amurka ya ƙera rigar da ba ta bukatar wanki ko da mutum zai rika saka ta na tsawon wata guda

HercLeon, wanda a baya ya ƙera kayan sawa da ya ce suna taimakawa wajen rage wari, ya bayyana HercShirt V5.0 a matsayin rigar da za ta iya daɗewa fiye da rigunan da ake wankewa akai-akai.

Tinubu ya sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya — Shugaban NRS Zacch Adedeji

Ya kawo misalin Andy Burnham na Birtaniya, inda ya ce ya ɗauki matakai da suka haɗa da rage haraji kan wutar lantarki ta gidaje da kuma rage kuɗin sufuri domin sauƙaƙa wa jama’a.

Akalla makarantun firamare da sakandare 65 sun daina aiki ko aka rufe a Arewacin Najeriya saboda rashin tsaro -rahoto

makarantun suna jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatun yara a wasu sassan Katsina da Adamawa.

Mun shafe fiye da shekara uku muna soyayya, amma tsadar rayuwa ta hana mu aure  – inji ma’auratan da aka yi wa Auren Gata...

Ta ce tana matukar son mijinta, kuma tana fatan za su rayu cikin zaman lafiya da fahimtar juna, tare da gina aure da wasu za su yi koyi da shi.

Kanun Labarai

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su

Rayuwa a Sambisa: Tsoffin mayakan Boko Haram sun bayyana yadda aka yaudare su - Dole ne al'umma ta yi hakuri ta karbe su, domin idan ba haka ba, akwai yiwuwar wasu su koma daji. - Hukumomi

Masu Karbar Albashin N150,000 zuwa N250,000 sun fi jin radadin tsadar rayuwa a Yuli -CBN

Bankin ya ce abubuwan da suka fi shafar yadda ’yan Najeriya ke kallon hauhawar farashi sun hada da tsadar makamashi da sufuri, rashin tsaro, matsalolin ababen more rayuwa, canjin kudin musayar waje da kuma ayyukan ’yan tsaka-tsaki.

Rashin Wuta Bayan 7 Na Yamma Na Sa ’Yan Najeriya Ƙara Haihuwa  — Fayose

Rashin Wuta Bayan 7 Na Yamma Na Sa ’Yan Najeriya Ƙara Haihuwa, Saboda suna komawa gida da wuri su kasance tare da matansu  — Fayose
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img