“Idan Laifi Ne, Ku Kama Dukanmu” – ‘Yan Najeriya Sun Fara Gasar Sanya Rigunan ‘Tinubu Must Go’ bayan kama matasa a Borno
Daga Wakiliya
Ana ci gaba da samun martani daga ‘yan Najeriya bayan da aka zargi ‘yan sanda sun kama tare da gurfanar da mutane biyar a Maiduguri bisa zargin sanya T-shirts masu dauke da rubutun “Tinubu Must Go.”
‘Yan sanda sun zargi mutanen da kokarin tunzura tarzoma, tayar da hankalin jama’a, bayan an ce sun buga tare da sanya T-shirts din a yankin West End Roundabout dake Maiduguri.
Mutanen biyar sun musanta zarge-zargen, yayin da kotu ta dage sauraron bukatar belinsu zuwa 6 ga Oktoba, 2026.
Lamarin ya haifar da martani a sassa daban-daban na Najeriya, inda wasu ke sanya irin wadannan T-shirts tare da cewa: “Idan sanya ‘Tinubu Must Go’ laifi ne, ku fara kama dukanmu.”
Amnesty International ta kuma yi kira da a saki mutanen biyar tare da janye tuhumar da ake yi musu, tana mai cewa bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana ba laifi ba ne.




