Hare-haren ’yan bindiga ya kashe mutane fiye da 10,000 cikin shekaru biyu na gwamnatin Tinubu – Amnesty

A shekara Biyun farko da hawan Tinubu mulki an kashe akalla mutane sama da 10,000 a jihohi bakwai – Amnesty

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Amnesty International ta ce a cikin shekaru biyu na farko na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, aƙalla mutane 10,217 ne aka kashe a hare-haren ’yan bindiga a jihohin Benue, Niger, Katsina, Kebbi, Plateau, Sokoto da Zamfara.

A cewar ƙungiyar, jihar Benue ce ta fi yawan adadin waɗanda aka kashe, sai jihar Plateau wadda aka kashe mutane 2,630.

Amnesty ta ce yanzu fiye da shekaru uku kenan da Shugaba Tinubu ya hau mulki da alkawarin inganta tsaro, amma matsalar tsaron ƙasar ta ƙara tsananta.

Ƙungiyar ta zargi hukumomin Najeriya da gazawa wajen kare haƙƙin rayuwa, lafiyar jiki, ’yanci da tsaron dubban mutane a sassan ƙasar.

Ta kuma ce a cikin shekaru biyu na farko na gwamnatin Tinubu, wasu sabbin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun bayyana, ciki har da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da kuma Mamuda a jihar Kwara.

Amnesty ta ƙara da cewa ɗaruruwan ƙauyuka sun fuskanci hare-hare tare da tilasta wa mazauna barin gidajensu a jihohin Benue, Borno, Katsina, Sokoto, Plateau da Zamfara.

Ƙarin matsin rayuwa ga waɗanda suka rasa matsugunansu

Ƙungiyar ta ce yawaitar hare-haren na ƙara jefa ƙasar cikin barazanar fuskantar matsalar jinƙai.

A cewar Amnesty International, yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu a jihohin Plateau da Katsina sun shaida mata cewa dole sai sun nemi taimakon jama'a domin samun abin da za su ci da gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

A gundumar Dangulbi da ke jihar Zamfara kuma, manoma na kallon amfanin gonarsu, musamman dankalin Hausa, yana lalacewa saboda ’yan bindiga sun hana su kai kayan amfanin gonar kasuwa mafi kusa.

Amnesty ta ce a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan Adam, hukumomi na da alhakin kare rayukan jama'a da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ake zargi da hannu a kashe-kashen.

Ta ce hukumomin Najeriya suna kuma da alhakin tabbatar da cewa waɗanda hare-haren suka shafa sun samu damar neman adalci da kuma diyya ko wasu hanyoyin magance matsalolin da suka fuskanta.

Ƙungiyar Amnesty International Nigeria ce ta wallafa bayanan.

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Tinubu za ta dawo da binciken mai a Arewa bayan tsaida aikin tun bayan hawansa mulki 

Shugaban RMAFC ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na damuwa da yadda aikin ya tsaya, yana mai cewa an ba gwamnonin Bauchi da Gombe tabbacin cewa za a sake tura kayan aiki da ma'aikata domin ci gaba da aikin.

Duk wanda ya ce bai amfana da tallafin Tinubu ba, to baya Najeriya – Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu 

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaben Bola Tinubu a 2027, yana mai cewa yana da yakinin shugaban zai ci gaba da kawo sauyi a kasar.

Murna Ta Koma Ciki: Tinubu ya janye sunayen kwamitin yakin neman zaɓensa na 2027 da APC ta fitar ya sa a sake gyare-gyare

Yanzu dai ana sa ran sabon jerin kwamitin zai ƙara wakiltar sassa daban-daban na jam’iyyar tare da shigar da manyan jiga-jiganta kafin fara babban yaƙin neman zaɓen 2027.

Maza ba wawaye bane: Ba za ki yi wa mijinki rashin kunya sannan ki sa ran zai ci gaba da sonki ba – Zainab

Jamiu Zainab ta ce wasu mata ba sa son a yi musu gyara, kuma kan yi gardama ko mayar da magana idan mazajensu suka yi magana da su.

Zan yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya zarce a 2027 –  Christopher Musa ya karɓi naɗin da APC ta yi masa

Janar Christopher Musa ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kasance cikin haɗin kai, yana mai cewa yana da yakinin APC za ta yi nasara a zaɓen 2027 tare da ci gaba da inganta shugabanci da tsaro a ƙasar.

Kanun Labarai

Tinubu Zai Ci Zabe Kuma APC za ta ci gaba da mulkar Najeriya har bayan 2031 -inji Yari 

Yari ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, yana ganin ayyukan gwamnatin cikin shekaru uku da suka gabata za su taimaka wa APC wajen samun ƙarin wa’adi.

Kamfanin Dangote ya faɗaɗa kai man fetur kyauta zuwa Kano da wasu jihohi domin saukar da farashin man a gidajen mai

Ana sa ran rage kuɗin safarar man fetur zai ba ‘yan kasuwa ƙarin damar sauke farashin man a gidajen mai, idan aka samu ci gaba da rage kuɗaɗen da ke cikin tsarin rarraba man.

Maido da Tallafin Man Fetur (Subsidy) zai mayar da Najeriya baya, ya jefa mutane a wahala – Idris

Sai dai ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar wahalhalu sakamakon sauye-sauyen, amma ya ce dawo da tallafin man fetur ba mafita ba ce.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img