Tinubu ya bai wa Famadewa ragamar tsara sabon tsarin tsaron Najeriya na shekaru biyar

Tinubu ya bai wa Famadewa ragamar tsara sabon tsarin tsaron Najeriya na shekaru biyar – abin da ya sake jawo tambayar ‘wanene Oga?’ tsakaninsa da NSA Nuhu Ribadu

Daga Wakiliya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa, ragamar jagorantar aikin tsara sabon tsarin tsaron Najeriya na shekaru biyar.

Wannan mataki ya sake jawo tambayar da aka dade ana yi tun bayan naɗin Famadewa kan yadda aikinsa zai kasance a ƙarƙashin Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu – musamman kan batun wanda ke da babban iko ko jagoranci a wasu harkokin tsaro.

A sabon tsarin da Shugaba Tinubu ya amince da shi, an ɗora wa Famadewa alhakin daidaita aikin da kuma samar da sakatariyar kwamitin da zai tsara cikakken binciken barazanar tsaro na ƙasa da kuma shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar.

Mambobi: An kafa kwamitin ne da manyan jami’an tsaro da suka haɗa da Nuhu Ribadu, Ministan Tsaro Janar Christopher Musa, Karamin Ministan Tsaro Bello Muhammad Matawalle, Shugaban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede, da shugabannin rundunonin soji.

Sauran mambobin sun haɗa da Shugaban Rundunar Ƙasa Laftanar Janar Waidi Shaibu, Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, Shugaban Rundunar Sojin Ruwa Vice Admiral Idi Abbas, Darakta-Janar na DSS Tosin Ajayi, da Darakta-Janar na NIA Ambasada Mohammed Mohammed.

Sabon tsarin zai ƙunshi National Threat Assessment, wato cikakken binciken manyan barazanar tsaron Najeriya, da kuma hanyoyin magance su na shekaru biyar.

Shugaba Tinubu ya ce manufar shirin ita ce samar da tsarin bai ɗaya da zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano barazanar ƙasa, tsara abubuwan da suka fi muhimmanci da kuma daidaita yadda ake amfani da sojoji da sauran jami’an tsaro.

Ya ce ko da yake ayyukan tsaro na baya-bayan nan sun samu wasu nasarori, har yanzu akwai bukatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Shugaban ya ba kwamitin kwanaki 90 domin kammala aikin da gabatar da shi gare shi domin amincewa.

Sai dai sanarwar ba ta ce Famadewa ya zama sama da Nuhu Ribadu a tsarin shugabancin harkokin tsaron ƙasa ba. Abin da ta bayyana shi ne cewa Famadewa ne aka ba alhakin daidaita wannan takamaiman aikin, yayin da Nuhu Ribadu yake cikin mambobin kwamitin.

Saboda haka, matakin ya sake mayar da hankali kan yadda za a raba ayyuka da iko tsakanin ofishin NSA da sabon ofishin mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaron cikin gida.

DA DUMI-DUMI

Bai kamata addini ya zama ma’aunin zaɓe a Najeriya ba domin a tsarin dimokuraɗiyya, tikitin Musulmi da Musulmi, Kirista da Kirista, Musulmi da Kirista...

Ya ce da a ce Najeriya tana tafiyar da mulkin Shari’a yadda Alƙur’ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) suka tanada, to Musulmi ne kaɗai za su iya neman shugabanci.

Tun kafin Aurenmu nasan ba zai yi ƙarko ba – Halima tsohuwar matar Bashir El-Rufai ta yi magana kan rayuwarta bayan rabuwar aurensu

Bashir ya sanar da rabuwar a lokacin, inda ya yi amfani da kalmar “Gen Z wahala”. Daga baya ya nemi afuwa kan yadda ya sanar da batun.

An cire wa wani mutum dutse mai nauyin kilogiram 3.1 daga mafitsararsa a Sri Lanka

Duwatsu a mafitsara na samuwa ne lokacin da fitsari ya dade yana zama a cikin mafitsara, lamarin da ke sa wasu sinadarai da ke cikinsa su taru su zama dutse.

Dukan yara a matsayin horo na iya sa su fanɗare su zama mugaye idan sun girma -inji Masana

Ta ce saboda haka, horon da ya fi mayar da hankali kan fahimtar kuskure da koyar da yaro abin da ya dace na iya zama mafi amfani fiye da hukuncin da ke jawo tsoro kawai.

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi ‘tagging’ Shugaban New York, yana korafi a gyara wasu ramuka da ya gani – kafin ya...

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi 'tagging' Shugaban New York Mamdani, yana korafi a gyara wasu manyan ramuka da ya gani – kafin ya je aiki ya dawo har an gyara

Kanun Labarai

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.

Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar -Wike

Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img