Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi ‘tagging’ Shugaban New York, yana korafi a gyara wasu ramuka da ya gani – kafin ya dawo gida daga aiki har an gyara

Wani matashi a birnin New York na Amurka ya wallafa wani bidiyo a TikTok yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa aiki, inda ya tagging din Shugaban Birnin (magajin birnin New York din), Zohran Mamdani, tare da neman a gyara manyan ramukan da ke wata hanya.

Abun mamaki ko da ya dawo daga aiki daga baya a wannan rana, sai ya tarar an cike ramukan. Inda ya yi Bidiyo kuma bidiyon ya bazu sosai a shafukan sada zumunta.

Na ci karo da bidiyon ne a TikTok, amma abin da ya fi bani dariya shi ne yadda wasu ’yan Afirka, musamman ’yan Najeriya, suka mayar da martani.

Wani ya ce: “Da a Najeriya wannan abu ya faru, da kama shi za a yi.”

Wani kuma ya ce: “Da a Najeriya wani Data Boy zai taso shi gaba da zagi, ya zarge shi da bata wa kasar suna.”

Wani dan Uganda kuwa ya ce: “Da a Uganda wannan ya faru, da gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti domin binciken ramukan. Kudin zaman kwamitin da alawus dinsa kuwa da ya fi kudin cike ramukan.”

Amma bayan barkwancin, akwai darasi mai muhimmanci a ciki.

Ya kamata ’yan kasa su iya nuna matsalolin da ke cikin al’ummominsu ba tare da tsoron a hukunta su ba. Haka kuma, ya kamata gwamnati ta dauki irin wadannan korafe-korafe a matsayin bayanan da za su taimaka wajen gyara matsaloli, ba wai ta kalli abun a matsayin kai mata hari ne ko kokarin bata mata suna ba.

— Fassarar Sharhin Ameer Lukman

DA DUMI-DUMI

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.

Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar -Wike

Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”

APC ta zargi an yi mata magudin zaɓe a Osun, ta nemi a sake duba sakamakon

Sai dai APC ta ce tana ci gaba da duba sakamakon da yadda aka gudanar da zaɓen, wanda zai iya zama matakin farko na ƙalubalantar sakamakon da aka sanar.

Wike ya umarci a rushe duk gidajen da suka toshe hanyoyin ruwa a Abuja

Wike ya umarci rushe gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa a Abuja Daga Wakiliya  Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja. Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata. Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba. Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin 'yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa. Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja. Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,  Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar. Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.

Kanun Labarai

Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ daidai yake da kisan kai — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.

Ya Allah Ka Kare Mu Daga Maza Azzalumai – labarin wata maijego da na gani a asibiti ya girgiza ni

Ta haihu babu ko tsinke na haiuwa daga mijin, ya ki rako ta Asibiti, babu wani nashi kuma ko sisi bai bayar ba, ita ce matar shi ta huɗu, haihuwa na 11, yan uwanta suke komai, tana cikin nakuda ma sai da tayi mashi tuwo kafin ta taho Asibiti....

Fitaccen Jarumin Fim Nicolas Cage Ya Ce Yana Iya Tuna Abin da Ya Faru Tun Yana Cikin Mahaifiyarsa

Masana kimiyya sun ce yawancin mutane ba sa iya tuna abubuwan da suka faru kafin su kai kusan shekara biyu ko uku
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img