An kama ɗa da mahaifiyarsa kan zargin shirya kashe tsohon mijinta, uban ɗan nata, a Kano

An kama ɗa da mahaifiyarsa kan zargin shirya kashe tsohon mijinta, uban ɗan nata, a Kano

Daga Wakiliya

An kama wani mutum da mahaifiyarsa a Kano bisa zargin shirya kashe tsohon mijinta kuma mahaifinsa, Alhaji Usman Shanono, mazaunin unguwar Dantsinke.

Rahotanni sun ce mutumin da mahaifiyarsa, wadda tsohuwar matar Alhaji Shanono ce, shi kuma ɗansa ne, sun ɗauki wani mutum haya tare da ba shi N500,000 domin ya kashe Alhajin.

Sai dai mutumin da aka dauka hayar ya sanar da Alhaji Shanono, inda suka shirya dabarar yin kamar an kashe shi.

Makashin ya kai wa waɗanda suka ɗauke shi aikin agogon Shanono da wasu kayayyakin sa, lamarin da ya sa suka yi zaton ya kammala aikin da suka bashi.

Daga bisani aka fara sanar da mutuwar Alhaji Shanono tare da tattara masu makoki da shirin jana'izarsa wanda Ɗan nasa da tsohuwar matarsa suka halarta domin nuna nasu alhinin,

Sai dai kwatsam sai aka ga Alhaji ya bayyana wajen jana'izar tasa tare da jami'an tsaro, abin da ya kai ga kama ɗan nasa da tsohuwar matar tashi.

A yanzu haka mutanen biyu na fuskantar shari'a kan zargin hannu a yunkurin kashe shi.

An ruwaito lamarin ne a shirin In Da Ranka na Freedom Radio Kano.

Lamarin ya bar mutane cikin mamaki, musamman yadda ake zargin ɗan mutum da tsohuwar matarsa da hannu a wani shiri na kashe shi.

DA DUMI-DUMI

Zan so na rika fitowa a budurwa maimakon uwa a fim -in ji Rahama Sidi

Rahama Sidi ta ce harkar fim ta taimaka mata wajen cimma wasu nasarori a rayuwa, ciki har da mallakar mota da gida nata, tare da wasu abubuwa da dama da ta samu ta hanyar sana’ar.

ICPC ta gano jami’in da ya saka ‘yan uwansa 14 a albashin gwamnati, da kuma mai karbar albashi 13 shi kadai

Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.

Beli kyauta ne’ Idan aka nemi ku bayar da kudi, ku kira IGP’ — Rundunar ‘yan Sandan Najeriya

“Doka ba ta ba da damar wani ya biya kudi domin beli ba a kowane ofishin ‘yan sanda a Najeriya,” in ji shi.

Matatun man fetur din Najeriya za su dawo aiki – Tinubu

“Na karbi dukkan nauyin da ya shafi abin da ya faru a baya. Nauyin da ke kaina yanzu shi ne gyara tattalin arziki domin amfanin mafi yawan ‘yan Najeriya,” in ji shugaban.

Dan siyasar da ya rantse da Alƙur’ani zai ci gaba da biyayya ga Kwankwaso ya koma APC

Ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya kira rashin cika alkawura daga jam’iyyar, yana mai cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 a ƙarƙashin APC.

Kanun Labarai

Musulmi da Kiristoci sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja

Sun kuma jaddada cewa manufar yarjejeniyar ba wai hada addinai wuri daya ba ce, sai dai gina fahimtar juna da girmama bambance-bambance.

Ana tsare da El-Rufai ne saboda ya raba gari da Tinubu – Mataimakin Atiku – M/Atiku

Ya ce, “Wace irin shaida ake bukata don tabbatar da cewa ana yakar ‘yan adawa ne ba cin hanci da rashawa ba?”

Matar da ta shafe shekaru tana ƙaurace wa nama sai ganyayyaki ta fashe da kuka bayan ta ci nama karo na farko

Soo a wani dogon bidiyo ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta fara cin abinci marar nama ba wai kawai saboda kare dabbobi ko muhalli ba ne. Ta bayyana cewa tsawon shekaru tana kokarin rage kiba, kuma daga bisani tsarin vegan ya koma wani nau'in takura wa kanta wajen cin abinci saboda yadda take kallon jikinta.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img