An cire wa wani mutum dutse mai nauyin kilogiram 3.1 daga mafitsararsa a Sri Lanka

An cire wa wani mutum dutse mai nauyin kilogiram 3.1 daga mafitsararsa a Sri Lanka

Daga Wakiliya

Likitoci a wani asibiti a Sri Lanka sun yi nasarar cire wani babban dutse daga mafitsarar wani mutum mai shekaru 55, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 3.1.

Likitocin Asibitin Trincomalee District General Hospital ne suka yi aikin tiyatar a makon da ya gabata, inda suka cire dutsen da suka ce girmansa ya yi kama da ƙwan jimina.

Rahotanni sun ce mutumin yana kwance a asibitin ne bayan ya kamu da shanyewar jiki, amma yayin da ake kula da shi, likitoci suka lura yana fama da matsalar yin fitsari.

Binciken da aka gudanar ya gano cewa yana ɗauke da wani babban dutse a cikin mafitsararsa, lamarin da ya sa aka tura shi ga ƙwararrun likitocin tiyatar mafitsara.

Likitan mafitsara da ya jagoranci aikin, Dokta Pragaladhan Balakrishnan, ya ce dutsen yana da nauyin da ya yi daidai da na jaririn da aka haifa, kuma girmansa ya kai kusan santimita 17.

Ya ce mutumin yana cikin ƙoshin lafiya bayan an cire dutsen, kuma yana ci gaba da samun kulawa a asibitin saboda sauran matsalar lafiyarsa.

Dokta Balakrishnan ya ce, bisa ga bayanan da suke da su, wannan na iya zama dutse mafi girma da aka taɓa rubutawa kuma aka cire wa mutum ta hanyar tiyata.

Daraktar asibitin, Sandamali Samarakoon, ta ce akwai yiwuwar lamarin ya cancanci shiga littafin tarihin duniya na Guinness a matsayin dutse mafi girma da aka cire daga mafitsara ta hanyar tiyata.

A shekarar 2003 ne aka taɓa cire wani dutse mai nauyin kilogiram 1.9 daga mafitsarar wani mutum a Brazil, wanda Guinness World Records ya bayyana a matsayin mafi girma da aka taɓa samu a wancan lokacin.

Dutsen da aka cire a Sri Lanka ya fi wannan nauyi da kilogiram 1.2.

Duwatsu a mafitsara na samuwa ne lokacin da fitsari ya dade yana zama a cikin mafitsara, lamarin da ke sa wasu sinadarai da ke cikinsa su taru su zama dutse.

Ƙananan duwatsu na iya fita da kansu, amma manya na iya toshe hanyar fitsari kuma su buƙaci magani ko tiyata.

DA DUMI-DUMI

Dukan yara a matsayin horo na iya sa su fanɗare su zama mugaye idan sun girma -inji Masana

Ta ce saboda haka, horon da ya fi mayar da hankali kan fahimtar kuskure da koyar da yaro abin da ya dace na iya zama mafi amfani fiye da hukuncin da ke jawo tsoro kawai.

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi ‘tagging’ Shugaban New York, yana korafi a gyara wasu ramuka da ya gani – kafin ya...

Matashi ya yi bidiyo a TikTok ya yi 'tagging' Shugaban New York Mamdani, yana korafi a gyara wasu manyan ramuka da ya gani – kafin ya je aiki ya dawo har an gyara

Kocin Masar ya suma yayin da yake ƙoƙarin raba faɗa tsakanin matansa, daga bisani ya saki uwargidarsa

Hossam Hassan, tsohon ɗan wasan tawagar ƙasar Masar ne kuma wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin ƙasar. Ya fara horar da tawagar ƙasar a shekarar 2024.

Da kyar Tinubu ya amince da Osinbajo a matsayin mataimakin Buhari – ya dage sai an bai wa matarsa Oluremi

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya kuma ce lokacin da Buhari ya nemi goyon bayansa bayan taron APC na 2014, ya sharɗanta masa cewa kada ya tsaya da tikitin Musulmi da Musulmi.

Da Tinubu ya so APC ta ci zaɓen Osun ko ta halin ƙa-ƙa, da ni za a tura jihar -Wike

Ya ce: “Da Shugaban kasa na son cin zaben Osun da ko-ta-halin ƙa-ƙa, da na je can, kuma da mun ci zaben. Babu abin da gwamnan zai iya yi.”

Kanun Labarai

APC ta zargi an yi mata magudin zaɓe a Osun, ta nemi a sake duba sakamakon

Sai dai APC ta ce tana ci gaba da duba sakamakon da yadda aka gudanar da zaɓen, wanda zai iya zama matakin farko na ƙalubalantar sakamakon da aka sanar.

Wike ya umarci a rushe duk gidajen da suka toshe hanyoyin ruwa a Abuja

Wike ya umarci rushe gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa a Abuja Daga Wakiliya  Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci hukumomin birnin da su fara rushe gidajen da aka gina ko kuma suka tare hanyoyin ruwa a Abuja. Wike ya bayar da umarnin ne bayan ya duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama ranar Talata. Ya ce za a fara aikin nan take kuma za ayi ta aikin har zuwa ranar Asabar, ba tare da la'akari da masu gidajen ba. Ministan ya ce wasu daga cikin gine-ginen mallakin 'yan majalisa da wasu masu hannu da shuni ne, amma doka za ta shafi kowa. Ya ce gine-gine a kan hanyoyin ruwa, toshe magudanan ruwa da zubar da shara na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a Abuja. Wike ya kuma umarci hukumomin FCT da su gaggauta kwashe laka da datti daga magudanan ruwa a babban birnin,  Ya ce sauyin yanayi da yawan ruwan sama na taka rawa wajen ambaliyar, amma ayyukan mutane ma na kara tsananta matsalar. Ministan ya ce ba za a dakatar da rushe-rushen saboda ana cikin lokacin siyasa ba, yana mai cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da dokokin tsara birnin.

Daga yanzu ‘Daukar doka a hannu’ daidai yake da kisan kai — IGP Disu ya gargadi ’yan Najeriya

Ya gargadi mutanen da ke shirya ko tunzura jama'a, wadanda ke daukar hotuna ko bidiyon abin da ke faruwa su yada shi, da kuma wadanda ke hana ’yan sanda shiga tsakani ko kai agajin gaggawa kan wanda ake zargi, cewa su ma za su iya fuskantar tuhuma.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img