An kama wata Amarya bisa zargin sanya wa mijinta guba kwana 40 da aurensu a Bauchi

An kama wata Amarya bisa zargin sanya wa mijinta guba kwana 40 da aurensu a Bauchi

Daga Wakiliya

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wata Amarya mai shekara 19, Aisha Musa, bisa zargin yunkurin kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba a cikin abinci.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026, da misalin karfe 3:15 na rana a kauyen Gwamma da ke karamar hukumar Bauchi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya ce ana zargin matar, wadda aka ce kimanin kwanaki 40 kacal da aurensu, da sanya wani abu mai guba a cikin abincin mijinta.

Ya ce daga bisani, da misalin karfe 7:40 na yamma, wata mata da ke zaune a yankin Wunti Dada ta kira ’yan sanda tare da sanar da su abin da ya faru.

A cewar rundunar, jami’an ’yan sanda daga sashen ‘C’ na Tafawa Balewa Estate sun garzaya wurin, inda suka kai wanda abin ya shafa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin samun magani.

’Yan sandan sun ce mutumin na karbar magani kuma a halin yanzu yana samun sauki,

Rundunar ta ce an kama Aisha Musa, kuma a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta amsa zargin da ake mata.

Majiyar Wakiliya ta ruwaito an kuma kwato wata kwalbar da ake zargin an yi amfani da ita wajen ɓoye gubar, tare da ragowar abincin da ake zargin an sanya masa gubar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike.

Rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

’Yan sandan sun kuma bukaci jama’a da su rika taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

DA DUMI-DUMI

Ana cece-kuce bayan nada wata lauya Musulma a matsayin Alkaliyar kotu a Amurka

Hukumar garin Benoit ma ta tabbatar da cewa Ali ta cika sharuddan da dokar Mississippi ta tanada domin zama alkalin kotun karamar hukuma, tana mai cewa kasancewar mutum Musulmi ba ya hana shi rike irin wannan mukami.

An kama ɗa da tsohuwar matar babansa kan zargin shirya kashe mahaifinshi kuma tsohon mijinta a Kano

Sai dai kwatsam sai aka ga Alhaji ya bayyana wajen jana'izar tasa tare da jami'an tsaro, abin da ya kai ga kama ɗan nasa da tsohuwar matar tashi.

Zan so na rika fitowa a budurwa maimakon uwa a fim -in ji Rahama Sidi

Rahama Sidi ta ce harkar fim ta taimaka mata wajen cimma wasu nasarori a rayuwa, ciki har da mallakar mota da gida nata, tare da wasu abubuwa da dama da ta samu ta hanyar sana’ar.

ICPC ta gano jami’in da ya saka ‘yan uwansa 14 a albashin gwamnati, da kuma mai karbar albashi 13 shi kadai

Musa Aliyu ya ce hukumar za ta kara amfani da fasaha da bayanai wajen dakile cin hanci da kare dukiyar gwamnati, tare da mayar da hankali kan hana barna kafin faruwar ta.

Beli kyauta ne’ Idan aka nemi ku bayar da kudi, ku kira IGP’ — Rundunar ‘yan Sandan Najeriya

“Doka ba ta ba da damar wani ya biya kudi domin beli ba a kowane ofishin ‘yan sanda a Najeriya,” in ji shi.

Kanun Labarai

Matatun man fetur din Najeriya za su dawo aiki – Tinubu

“Na karbi dukkan nauyin da ya shafi abin da ya faru a baya. Nauyin da ke kaina yanzu shi ne gyara tattalin arziki domin amfanin mafi yawan ‘yan Najeriya,” in ji shugaban.

Dan siyasar da ya rantse da Alƙur’ani zai ci gaba da biyayya ga Kwankwaso ya koma APC

Ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon abin da ya kira rashin cika alkawura daga jam’iyyar, yana mai cewa yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027 a ƙarƙashin APC.

Musulmi da Kiristoci sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja

Sun kuma jaddada cewa manufar yarjejeniyar ba wai hada addinai wuri daya ba ce, sai dai gina fahimtar juna da girmama bambance-bambance.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img