Me ya sa za ku saka duk wanda kuka taɓa magana da shi sau ɗaya ko biyu a WhatsApp Group ɗin aurenku? – Mr. Abdul Reacts
….Bikin auranku alhakinku ne, ba alhakin jerin lambobin wayarku ba, – in ji shi.
Daga Wakiliya
Fitaccen mai sharhi, Mr. Abdul Reacts, ya soki yadda wasu mutane ke saka abokai da waɗanda ba su da kusanci da su cikin WhatsApp Groups din bikin aurensu, tare da matsa musu su bayar da gudunmawa,
Mr. Abdul Reacts ya ce ba daidai ba ne mutum ya yanke shawarar yin aure, sannan ya buɗe jerin lambobin wayarsa ya saka duk wanda ya taɓa magana da shi wani ma bai fi sau ɗaya ko sau biyu ba a WhatsApp Group dinsu ba tare da izininsa ba.
Ya ce daga nan sai a fara neman mutane su bayar da N50,000, N100,000 ko N200,000, alhali wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali na kuɗi kuma ba su da ko N10,000 a lokacin.
Ya bayyana cewa matsin lambar na iya sa mutane su ji kunya ko jin kaman sun yi laifi idan ba su bayar ba, saboda tsoron a ɗauke su a matsayin abokan banza ko waɗanda ba sa son ci gaban abokansu.
Mr. Abdul Reacts ya kuma ba da misalin wani Group din WhatsApp da aka taɓa saka shi a ciki, inda aka rika wallafa sunayen mutanen da suka biya kuɗi tare da yaba musu, abin da ya ce yana sanya sauran mutane jin cewa dole ne su biya domin a tabbatar da cewa su ma “abokai na gaskiya” ne.
Game da (Anko) Asoebi, ya ce wasu ma suna sanya farashin kayan da ya yi tsada, sannan su bayyana cewa sai wanda ya sayi kayan ne zai samu gayyatar zuwa bikin.
Ya ce hakan yana mayar da halartar aure tamkar kasuwanci, inda ake tilasta wa mutane kashe kuɗin da ba su shirya kashewa ba.
Mr. Abdul Reacts ya ce matasan Najeriya da dama kan taimaka wa akalla biki ɗaya kusan kowane wata, ko da kuwa ba su da hali, abin da ya kwatanta da wani nau'in “haraji” da ake biya saboda kasancewa cikin abokan hulɗa.
Sai dai ya jaddada cewa taimaka wa masoyi ko aboki da kuɗi abu ne mai kyau idan mutum ya yi hakan da son ransa kuma yana da hali.
“Amma da zarar ka fara matsa wa mutane, yi musu laifi ko amfani da abota wajen tilasta musu bayar da kuɗi, ka riga ka wuce gona da iri,” in ji shi.
A karshe ya ce, bikin auranka alhakinka ne, ba alhakin jerin lambobin wayarka ba.




