An nuna mani “wani babban dan siyasa zai mutu a Najeriya, kuma babu abunda za a iya akai” – Fasto Selman
Daga Wakiliya
Limamin Kirista ya ce ya ga mutuwar wani babban ɗan siyasar Najeriya a wahayi
Daga Wakiliya
Babban Fasto Joshua Selman ya ce ya samu wani ilhama da ya nuna masa mutuwar wani babban ɗan siyasar Najeriya, inda ya ce ya ga jama’a sun taru suna yi masa jana’iza.
Selman ya bayyana cewa ya samu wannan ilhamar ne yayin da yake addu’a ga marasa lafiya, kuma ya yi ta tunanin ko ya bayyana abin da ya gani ga jama’a ko a’a.
Ya ce ba ya fatan ya yi wannan magana, amma ya ji wani ƙarfi na ruhaniya da ya tilasta masa bayyana abin da ya gani.
“Ina ganin wani babban ɗan siyasa a wannan ƙasa. Lokacinsa ya ƙare. Ina ganin zai tafi, ina ganin mutane sun taru suna binne shi,” in ji shi.
Selman ya ce manufarsa ba ita ce murna da mutuwar ɗan siyasar ba, sai dai a cewarsa, domin iyalansa su shirya
Ya ƙara da cewa ba ya yin malumta domin burge mutane, yana mai cewa abin da ya faɗa ya fito ne daga abin da ya ce Allah ya sanya a zuciyarsa.
Sai dai Fasto Selman bai bayyana sunan ɗan siyasar da yake magana a kansa ba, kuma babu wata shaida da ya nuna mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari nashi.




