2027 ce damar ƙarshe ta Sarki Aminu? Shin magoya bayansa sun fara shirin amfani da ƙuri’unsu wajen kare sarautarsa?
Daga Wakiliya
Duk da cewa batun Sarautar Kano na gaban kotu, kuma ana sa ran za a yanke hukunci kan lamarin bayan babban zaɓen 2027, al’amuran da ke faruwa a Kano na ƙara sanya batun sarautar cikin siyasar jihar.
Masu bibiyar al’amuran Kano na ganin cewa Gwamnatin Jihar Kano karara tana nuna goyon baya da fifiko ga bangaren Sarki Sanusi, yayin da a lokuta da dama ake ganin Sarki Aminu ba ya samun irin wannan kulawa ko halartar manyan ayyukan gwamnati tare da shi.
Wannan yanayi ya fara sa wasu daga cikin magoya bayan Sarki Aminu yin kira da a yi anti-party a zaɓen 2027 – wato misali a mara wa jam’iyyar da ke mulki baya a zaɓen shugaban ƙasa, amma a zaɓen gwamna a zaɓi wata jam’iyya daban domin ƙalubalantar Gwamna Abba Kabir Yusuf da hana shi komawa kan kujerar gwamna.
Masu wannan ra’ayi na ganin cewa idan Abba Kabir Yusuf ya sake samun nasara a zaɓen 2027, akwai yiwuwar batun Sarautar Kano ya sake komawa kan teburin gwamnati, kuma a cewarsu, hakan na iya kai ga cire rawanin Sarki Aminu ko ma fitar da shi daga jihar Kano.
A yanzu haka, tambayar da ke gaban Sarki Aminu da magoya bayansa ita ce:
Me ya kamata su yi domin hana faruwar hakan?
Shin su shiga siyasar 2027 kai tsaye ta hanyar goyon bayan ɗan takarar da zai iya kayar da Abba Kabir Yusuf, ko kuma su mayar da hankali kan shari’a, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da sauran hanyoyin da za su iya kare matsayin Sarki Aminu? Kuma shin hakan zai yi tasiri?
Abin da ba za a iya musantawa ba shi ne, batun Sarautar Kano da siyasar 2027 na ƙara zama abubuwa biyu da ke da alaƙa sosai, kuma matakin da Sarki Aminu da magoya bayansa za su ɗauka kafin zaɓen na iya yin tasiri sosai kan makomar lamarin.




