Amurka za ta kama duk shugaban da ke safarar miyagun ƙwayoyi -inji Trump
Daga Wakiliya
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta kama duk wani shugaban ƙasa da aka samu yana safarar miyagun ƙwayoyi.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a duniya, inda ya kuma yi nuni da Shugaban Venezuela Nicolás Maduro.
Ya ce Amurka ba za ta yi wa duk wani shugaban duniya da ke da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi sassauci ba, tana kuma shirye ta ɗauki matakin doka a kansa.
Maganar Trump ta jawo muhawara a fagen diflomasiyya da kafafen yaɗa labarai na duniya.




