2027: TMG ta nemi Atiku, Obi, Makinde da Sowore su haɗa kai don kayar da Tinubu 

DA DUMI-DUMI

2027: TMG ta nemi Atiku, Obi, Makinde da Sowore su haɗa kai don kayar da Tinubu

Daga Wakiliya

Ƙungiyar Tinubu Must Go (TMG) ta nemi manyan ’yan adawar Najeriya, Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da Omoyele Sowore, su haɗa kai domin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027.

A wata wasiƙa da ƙungiyar ta aika wa ’yan siyasar, TMG ta ce ya kamata su ajiye burikansu su shiga tattaunawa domin samar da ɗan takarar da zai wakilci ’yan adawa baki ɗaya.

Ƙungiyar ta ce ta yi wannan kira ne bisa abin da ta bayyana a matsayin ƙalubalen tsaro da na tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.

TMG ta kuma ce ba za ta ayyana wanda ya kamata ya janye wa wani ko wanda ya kamata ya zama ɗan takarar haɗin gwiwar ba, tana mai cewa ya kamata shugabannin su yanke irin wannan hukunci ta hanyar tattaunawa.

Ta ce tana shirin gudanar da tuntuba da magoya bayanta a ranar 24 ga Satumba domin jin ra’ayinsu kan wanda za su iya mara wa baya idan aka samu buƙatar haɗa tsarin siyasar ƙungiyar wuri guda.

Kiran ya zo ne yayin da ƙungiyoyi daban-daban ke ci gaba da ƙoƙarin ganin manyan ’yan adawa sun cimma matsaya kan ɗan takara guda gabanin zaɓen 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img