Ɗan Najeriya Ya Amsa Laifin Tura Dala Miliyan 1.64 Kuɗin Gwamnati zuwa Asusun Iyalansa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Wani ɗan Najeriya mazaunin Amurka, Adebanjo Popoola, ya amsa laifin karkatar da kusan dala miliyan 1.64 na kuɗaɗen gyaran gine-ginen gwamnati zuwa asusun bankin kansa da na iyalansa.

Popoola, mai shekaru 57, ya amsa laifuka uku na damfarar kuɗi ta hanyar sadarwa (wire fraud) a wata kotun tarayya da ke birnin St. Louis.

Masu gabatar da ƙara sun ce ya yi amfani da mukaminsa na jami’in duba gine-gine wajen bai wa kamfanonin da matarsa da ‘yar uwarsa suka kafa kwangiloli na miliyoyin daloli, duk da cewa wasu ayyukan ba a kammala su ba ko kuma ba a yi su yadda ya kamata ba.

Bincike ya nuna cewa an karkatar da kuɗin wajen biyan bashin gida, sayen motoci, tafiye-tafiye, bikin aurensa a Hawaii, caca da sauran kashe-kashe na jin daɗi.

Ana sa ran kotu za ta yanke masa hukunci a ranar 6 ga Oktoba, inda kowace tuhumar damfarar kuɗi ke ɗauke da hukuncin daurin shekaru har 20 a gidan yari tare da tara, baya ga mayar da kuɗaɗen da aka karkatar.

#Wakiliya | Muryar Arewa a Duniya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img