Kada Ka Kashe Kanka Don Neman Faranta Wa Mace Rai, Iya Wa Mata Sai Allah -inji Malamar Aji

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Fitacciyar malamar addini kuma mai ba da shawara kan zaman aure, Funke Felix-Adejumo, ta shawarci maza masu aure da kada su takura wa kansu ko su sadaukar da rayuwarsu wajen ƙoƙarin faranta wa matansu rai.

Da take jawabi a taron Recharge Conference, ta ce babu wani namiji da zai iya gamsar da mace gaba ɗaya, saboda dabi’ar mata ita ce son ganin abubuwa sun fi yadda suke.

Ta ce maza su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kula da iyalansu, amma kada su kai ga lalata lafiyarsu ko rayuwarsu saboda hakan.

Hakazalika, ta buƙaci mata su nemi hanyoyin samun kuɗin kansu maimakon dogaro kacokan da mazajensu, tana mai cewa mace ya kamata ta kasance tana da nata abin hannu domin ta ma iya yi wa mijinta kyauta da mamaki.

A cewarta, rayuwar mace bai kamata ta tsaya kan jiran abin da mijinta zai kawo ba, illa ta kasance mai cin gashin kanta ta fuskar tattalin arziki.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img