Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

DA DUMI-DUMI

Wani mutum ya rasa ransa bayan an yi masa dukan tsiya sakamakon zargin cewa yana bibiyar matar wani a Jihar Kano.

 

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa wanda ake zargin mijin matar ne ya shirya tarko domin kama mutumin. Bayan an kama shi, an yi masa jina-jina, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

 

A cewar Rundunar, an kama mijin, matarsa da kuma wani mutum guda, kuma a halin yanzu suna tsare a hannun ‘yan sanda yayin da ake tuhumarsu da zargin kisan kai.

 

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu idan bincike ya kammala.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img