Kifi na iya ɗaukar watanni da dama a cikin firiza ba tare da ya lalace ba, amma tsawon lokacin ya danganta da irin kifin, yawan kitsensa da kuma yadda aka nade shi kafin a saka a firiza.
Masana abinci sun bayyana cewa kifaye masu kitse irin su salmon, tuna da sardine kan fi dacewa a cinye su cikin watanni uku, yayin da kifaye marasa kitse irin su halibut za su iya kaiwa watanni shida idan an adana su yadda ya kamata.
Sun kuma ce idan an yi amfani da vacuum seal wajen nade kifin, wanda ke cire iska gaba ɗaya, kifin na iya kasancewa cikin inganci har na shekara guda a firiza.
Masanan sun shawarci mutane su cire iska daga cikin leda kafin su daskarar da kifi domin kauce wa freezer burn, wanda ke lalata ɗanɗano da ingancin naman kifin.
Haka kuma, ba a ba da shawarar a riƙa sake daskarar da kifin bayan an narke shi ba, saboda hakan na sa naman kifin ya yi laushi kuma ya rasa ingancinsa.
Idan kifin ya fara fitar da wani wari mai kama da na kakin zuma (crayon) yayin da yake firiza, hakan na iya nuna cewa ingancinsa ya lalace duk da cewa ba lallai ne ya zama haɗari ga lafiya ba.
Masana sun ce mafi dacewar wajen ajiye kifi a firiza shi ne ɓangaren baya, inda sanyi ya fi ƙarfi kuma ba ya yawan sauyawa lokacin buɗe ƙofar firiza.





