Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

DA DUMI-DUMI

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Wata mata da ake zargi ta yanke gaban saurayinta gaba ɗaya bayan ya bayyana mata cewa yana shirin auren wata mace, lamarin da ya jefa saurayin cikin mawuyacin hali.

 

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

A cewarsa, saurayin na kwance yana karɓar magani a asibiti, yayin da aka tsare matar da ake zargin a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sandan Kano da ke Bompai domin ci gaba da bincike.

 

CSP Kiyawa ya ce rundunar za ta fitar da cikakken bayani kan lamarin bayan kammala binciken da ake yi.

 

Wakiliya na bibiyar wannan lamari, kuma za ta kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu sabbin bayanai.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img