Uba Ya Kai Ƴarsa Mai Shekara 27 Kotu, Ya Roƙi a Tilasta Mata Yin Aure

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Wani mutum mai suna Lawal Hamisu, mahaifin yara 11, ya kai ƙarar ‘yarsa Fatima Lawal a gaban Kotun Shari’a ta II da ke Magajin Gari a Kaduna, inda ya roƙi kotu ta umarce ta da ta nemo miji domin a aurar da ita.

Lawal Hamisu ya bayyana wa kotun cewa Fatima mai shekara 27 ce kuma ta kammala karatun Higher National Diploma (HND).

A cewarsa, duk da cewa tana da masu zawarcinta, amma har yanzu ta ki fito da tsayayye,

Ya kuma zargi mahaifiyar Fatima da cusa mata ra’ayin da ya sa ta kauce masa, yana mai cewa, “Ta nemo wanda zai aure ta, ta gabatar da shi a kotu, kotu ta aurar da ita.

“Da take kare kanta, Fatima Lawal ta shaida wa kotun cewa a halin yanzu ba ta da wani tsayayyen saurayi da ya nemi aurenta, tana mai cewa duk masu zawarcinta ba su kai ga neman aurenta ba.

Alƙalin kotun, Malam Yakubu Abdullahi, ya bayyana cewa shari’ar tana da sarkakiya saboda ta shafi uba da ‘yarsa.

Ya ce zai gana da kowannensu a keɓance domin jin cikakken bayani kafin yanke hukunci.

Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Agusta domin yanke hukunci.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img