Matsalar Afirka Ita Ce Ƙarancin Yarda da Kai -Shugaba Museveni Ya Soki Kwaikwayon Turawa da Larabawa

DA DUMI-DUMI

“Matsalar Afirka Ita Ce Ƙarancin Yarda da Kai” – Shugaba Museveni Ya Soki Kwaikwayon Turawa da Larabawa

Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni, ya ce ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana nahiyar Afirka ci gaba ita ce ƙarancin yarda da kai da wasu ‘yan Afirka ke nunawa.

Museveni ya bayyana cewa wasu Kiristocin Afirka suna ɗaukar cewa zama Kirista na nufin su zama kamar Turawa, yayin da wasu Musulmai kuma suke ganin dole ne su kwaikwayi Larabawa.

A cewarsa, addini bai kamata ya sa mutum ya yi watsi da al’adunsa ko asalinsa ba, yana mai jaddada cewa ‘yan Afirka su riƙe martabarsu tare da kiyaye al’adunsu, ko da suna bin addinin Kirista ko Musulunci.

Kalaman nasa sun sake tayar da muhawara kan batun al’ada, addini da kuma yadda ‘yan Afirka ke kallon asalinsu a duniyar yau.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img