Daga Wakiliya
Shugaban ƙasar Nicaragua, Daniel Ortega, ya bayyana cewa ba za a sake gudanar da wani zaɓe a ƙasar ba, yana mai cewa gwamnatinsa na shirin samar da dokokin da za su hana abin da ya kira yunƙurin juyin mulki da cin amanar ƙasa.
Ortega, mai shekaru 80, ya yi wannan jawabi ne yayin bikin cika shekara 47 da juyin juya halin Sandinista da ya hambarar da gwamnatin Anastasio Somoza a shekarar 1979.
Tun daga shekarar 2007, Daniel Ortega ke mulkin Nicaragua, kuma an sha zarginsa da sauya dokoki domin tsawaita zamansa kan mulki.
A bara ma, an tsawaita wa’adin shugaban ƙasa zuwa shekara shida tare da ɗaga matarsa, Rosario Murillo, daga mataimakiyar shugaban ƙasa zuwa matsayin karamar shugabar ƙasa (Co-President).
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun dade suna zargin gwamnatin Ortega da murƙushe ‘yan adawa, kama masu fafutuka, ‘yan jarida da jagororin siyasa, musamman a zaɓukan shekarun 2011, 2016 da 2021.
A jawabinsa, Ortega ya ce za su yi aiki da Majalisar Dokoki wajen samar da dokokin da za su “gina katanga” domin hana waɗanda ya kira masu shirya juyin mulki sake samun damar karɓar mulki ta hanyar zaɓe.Haka kuma, Ortega ya soki gwamnatin Amurka kan abin da ya yi iƙirarin cewa ta aikata wa shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, yana zargin Amurka da kai farmaki fadar shugaban ƙasa tare da kama Maduro.
Sai dai babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan iƙirari.





