Rikicin ADC Ya Ƙara Tsananta: Nafiu Bala Ya Ce Ya Sanya Sunayen ‘Yan Takararsa a Shafin INEC

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban tsagin jam’iyyar ADC da ke rikici da tsagin da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta, Hon. Nafiu Bala Gombe, ya ce ya kammala sanya sunayen ‘yan takarar tsaginsa a babban shafin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) domin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa a ranar Lahadi, Nafiu Bala ya bayyana cewa tsaginsa ya yi nasarar loda sunayen ɗan takarar shugaban ƙasa, mataimakinsa da kuma ‘yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Ya kuma yi ikirarin cewa ya samu lambar sirri (access code) da INEC ke bai wa jam’iyyun siyasa, inda ya ce ya yi amfani da ita wajen saka sunayen ‘yan takararsa, kamar yadda ya yi zargin tsagin David Mark ma ya yi.

Nafiu Bala ya ce wannan mataki na nuna ƙudurin tsaginsa na kare muradun waɗanda ya kira “mambobin asali da na gado” na jam’iyyar, tare da jaddada cewa ADC ƙarƙashin jagorancinsa za ta tsayar da ‘yan takara nagari domin samar da shugabanci nagari ga ‘yan Najeriya.

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Hukumar INEC ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar ko musanta ikirarin Nafiu Bala ba, haka kuma tsagin David Mark bai yi martani kan wannan sabon ikirari ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img